Cesare Maldini ya mutu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cesare Maldini ya yi wasa a Milan ya kuma horar da tawagar Italiya da ta Paraguay

Tsohon dan wasan Italiya mai tsaron baya Cesare Maldini ya mutu yana da shekara 84.

Maldini ya lashe kofunan Serie A guda hudu a Milan da kuma kofin zakarun Turai na farko da kungiayar ta lashe a shekarar 1963.

Daga nan kuma ya horar da Milan shekara biyu daga 1972 zuwa 1974.

Maldini ya kuma horar da tawagar kwallon kafa ta Italiya a 1996, inda dansa Paolo shi ne kyaftin din tawagar.

Kociyan ya kuma horar da tawagar kwallon kafa ta Paraguay, inda ya jagorance ta gasar cin kofin duniya da aka yi a 2002.