Leicester ta doke Southampton da ci 1-0

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Leicester ta bai wa Tootenham wadda ke mataki na biyu a kan teburi tazarar maki bakwai

Leicester City ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburin Premier, bayan da ta doke Southampton da ci daya mai ban haushi a karawar da suka yi ranar Lahadi.

Leicester City ta ci kwallon ne ta hannun mai tsaron bayanta Morgan saura minti bakwai a tafi hutun rabin lokaci.

Da wannan nasarar da Leicester ta samu ya sa tana nan a matsayinta na daya a kan teburin gasar da maki 69 daga wasanni 32, Southampton kuwa tana mataki na bakwai da maki 47.

Leicester za ta ziyarci Sunderland ne a wasan mako na 33, yayin da Southampton za ta karbi bakuncin Newcastle United.