Manchester United ta ci Everton 1-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United tana mataki na biyar a kan teburin gasar Premier

Manchester United ta samu nasara a kan Everton da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 32 da suka kara a Old Trafford ranar Lahadi.

Anthony Martial ne ya ci wa United kwallon bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci wanda hakan ya ba ta damar samun maki uku rigis a karawar.

Kafin a fara wasan sai da aka yi bukin radawa kudancin filin wasa na Old Trafford sunan tsohon dan kwallon United, Sir Bobby Charlton.

Da kuma wannan sakamakon da United ta samu, ya rage saura maki daya tsakaninta da Manchester City wadda ke mataki na hudu a kan teburin Premier.

United din za ta fafata ne da Tottenham wadda ke matsayi na biyu a kan teburi a wasan mako na 33 ranar Asabar.