Real Madrid ta takawa Barcelona burki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barcelona tana nan a matakinta na daya a kan teburin La Liga

Real Madrid ta kawo karshen tsawaita wasanni 39 a jere da Barcelona ta yi ba a doke ta ba a dukkan fafatawa da ta yi a gasar wasannin bana.

Madrid din ta samu nasara ne a kan Barcelona da ci 2-1 a gasar La Liga wasan mako na 31 da suka yi a ranar Asabar a Camp Nou.

Tun kafin karawar Barcelona ta yi wasanni 39 a jere ba a doke ta ba a dukkan wasannin bana, inda ta ci guda 32 ta kuma yi canjaras a fafatawa bakwai.

Rabon da a doke Barcelona tun rashin nasarar da ta yi a hannun Sevilla da ci 2-1 a gasar La Liga ranar 3 ga watan Oktoban 2015.

Jumulla Barcelona ta ci wasanni 38 daga fafatawa 52 da ta yi a dukkan wasannin kakar nan, inda ta yi canjaras 10 aka kuma doke ta a karawa hudu.

Duk da rashin nasararta Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a teburin na La liga da maki 76 a wasanni 31, ita kuwa abokiyar hamayyar tata Real Madrid tana mataki na uku da maki 69.