Shaw ya koma yin atisaye a Man United

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shaw ya yi jinyar watanni tara, bayan da ya karye a wuri biyu

Mai tsaron bayan Manchester United, Luke Shaw, ya koma yin atisaye a ranar Litinin a karon farko tun raunin da ya ji kusan watanni bakwai da suka wuce.

Shaw ya karye a wuri biyu a lokacin da PSV Eindhoven ta doke United a gasar cin kofin zakarun Turai.

Juan Mata ne ya sanar da komawar Shaw atisaye a shafinsa na sada zumunta inda ya saka hotonsa a Instagram.

Kociyan tawagar kwallon kafar Ingila, Roy Hodgson ya ce har yanzu dan wasan yana da damar da zai iya murza wa Ingila tamaula a gasar cin kofin nahiyar Turai.