An soke jan katin da aka bai wa Kouyate

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kouyate zai buga wasan da West Ham za ta yi da Arsenal a Emirates ranar Asabar.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, ta soke jan katin da aka bai wa dan wasan West Ham United, Cheikhou Kouyate.

An kori dan wasan ne dan kasar Senegal a minti na 67 bisa cewar ya yi wa Dwight Gayle na Crystal Palace keta a karawar da suka yi a gasar Premier.

A lokacin da aka sallami dan kwallon, West Ham ta ci Crystal Palace 2-1, kafin a kammala fafatawar Palace ta farke kwallon da aka zura mata wasa ya tashi 2-2.

Da wannan hukuncin da aka yanke Kouyate zai buga wa West Ham gasar Premier da za ta kara da Arsenal ranar Asabar a Emirates.

Wani kwamiti ne mai zaman kansa da hukumar kwallon kafa ta Ingila ta kafa ya ce an kori dan kwallon ne bisa kuskure.