Chelsea: Naɗin Conte ba alkairi ba ne — Sutton

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Antonio Conte, sabon kocin Chelsea.

Tsohon dan wasan Chelsea, Chris Sutton ya ce naɗa Antonio Conte a matsayin sabon kociyan kulob din bai ba da wata ma'ana ba.

Sutton dai yana alaƙanta Conte da Jose Mourinho wanda aka kora a watan Disamba bisa zargin rashin shiri da 'yan wasa.

Mista Sutton ya ce " idan dai har a zamanin Mourinho 'yan wasa sun yi yajin aiki, to hakan zai iya faruwa a lokacin Conte ma."

Conte, mai shekara 46, zai fara jagorancin kulob din bayan kammala gasar Euro 2016.