Ebola zai dambata da Mai Takwasara a Sokoto

Image caption Ebola ne ya buge Mai Takwasara a karawar da suka yi a Zaria

Kungiyar wasan damben gargajiya ta kasa Nigeria, ta shirya gagarumin wasa da za a yi a Sokoto a cikin wannan watan.

Shugaban kungiyar Ali Zuma ya ce sun zabi yin wasa a Sotoko ne, bayan da aka kammala wadda aka yi a birnin Minna a watan jiya.

Ana sa ran Ebola dan damben Kudu zai halarci wasan, domin bai wa Mai Takwasara fansar kisa.

A cikin watan Fabrairu ne a birnin Zaria Ebola, ya buge Mai Takwasara, a turmi na biyu a lokacin Ajon Anas Dan Sarkin Fawa.

Tuni kungiyar dambe ta jihar Kano karkashin jagorancin Dan Liti ta ce za ta ziyarci wasannin ne tare da 'yan wasa Ebola da kuma Shamsu Kanin Emi.