Dalung yana tattauna wa da NFF

Image caption Minista wasanni na Nigeria yana tattauna wa da NFF

Ministan wasanni na Nigeria, Barista Solomon Dalung, yana tattauna wa da mahukuntan hukumar kwallon kafa ta Nigeria a ranar Talata.

Dalung ya ce suna tattauna wa ne domin samo bakin zare kan koma baya da wasannin kwallon kafar Nigeria ke fuskanta musamman tawagar 'yan wasan Super Eagles.

Ministan ya ce batutuwa biyar za su duba mahimmai a taron, amma bai fadi abubuwan biyar din ba.

Nigeria ba ta samu gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da Gabon za ta karbi bakunci a badi ba.

Kuma karo na biyu kenan da kasar ba ta je wasannin kwallon kafar Afirka ba, domin ba ta halarci wadda aka yi a Equotorial Guinea ba a shekarar 2015.