'Klopp ba zai ragantawa Dortmund ba - Tuchel

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Klopp zai kara da kungiyar da ya jagoranta shekara bakwai

Kociyan Borussia Dortmund Thomas Tuchel, ya ce Jurgen Klopp ba zai raga musu ba, idan sun zo karawa a gasar Europa a ranar Alhamis.

Liverpool din za ta ziyarci Borussia Dortmund domin buga wasan farko na cin kofin zakarun Turai a ranar Alhamis a Jamus.

Kuma a ranar ne Klopp zai kara da tsohuwar kungiyar da ya horar da tamaula tsawon shekara bakwai, ya kuma dauki kofin Bundesliga biyu da ita.

Tuchel ya ce da zarar an hura usur din fara wasa, babu abinda Klopp zai bukata da ya wuce samun nasara a kanmu, mu ma haka muke fata a kansu.

Kocin ya kuma kara da cewar ba za a taba mancewa da gudunmowar da Klopp ya bayar a Dortmund ba.