Mbokani ya yi ritayar buga wa kasarsa kwallo

Image caption Mbokani ya ce bai ji dadi da abinda mahukuntan kasar jamhuriyar Congo suka yi masa ba

Dieumerci Mbokani, mai taka leda a Norwich City, ya ce ya yi ritaya daga buga wa Jamhuriyar Congo tamaula.

Dan wasan ya ce ya yanke hakan ne, bayan da hukumar kwallon kafar kasar ta ce za ta hukunta shi, sakamakon rashin halartar wasanninta biyu na neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da bai yi ba.

Mbokani bai halarci karawar da kasarsa ta yi da Angola ba, bayan da harin da aka kai filin jirgin sama na Brussels ya kusa rutsawa da shi.

Dan wasan mai shekara 30, ya ce ya ji takaici da shugaban hukumar kwallon kafar kasar Constant Omari, ya ce duk da hakan ya kamata ya ziyarci Kinshasa.

Mbokani ya ce bai son ya sake buga wa Jamhuriyar Congo tamaula domin sun yi masa rashin adalci.

Ya kuma ce tun lokacin da abun ya faru babu wanda ya kirashi ya jajanta masa ko taya shi jimami tun lokacin da abun ya faru.

Mutane 32 ne suka mutu a harin bam da aka kai a Brussels a ranar 22 ga watan Maris.