Newcastle United ta sanar da samun riba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Newcastle tana mataki na 19 a kan teburin Premier

Newcastle United ta sanar da samun ribar kudi sama da fam miliyan 32, bayan da aka cire haraji.

Kungiyar ta ce ta samu karin ribar da ta kai kudi sama da miliyan 13 fiye da wadda ta samu a bara.

Sai dai kuma Manajan Darakta, Lee Charnley ya ce ya kwana da sanin cewar magoya baya sakamakon wasanni suke bukata.

Newcastle tana mataki na 19 a kan teburi da maki 25 da kwantan wasa daya, za kuma ta ziyarci Southampton a ranar Asabar.