PSG da Manchester City sun tashi wasa 2-2

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption City za ta karbi bakuncin PSG a ranar Talata a Ettihad

Paris St Germain ta tashi wasa 2-2 da Manchester City a gasar cin kofin zakarun Turai wasan daf da na kusa da karshe da suka yi a Faransa ranar Laraba.

City ce ta fara zura kwallo ta hannun De Bruyne a minti na 38 da fara tamaula, kuma saura minti hudu a tafi hutun rabin lokaci PSG ta farke kwallo ta hannun Ibrahimovic.

Bayan da aka dawo daga hutun ne Rabiot ya ci wa PSG kwallo na biyu, kuma Fernandinho ya farke wa City kwallon da aka zura matan.

Wannan ne karon farko da Manchester City ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar ta zakarun Turai.

Manchester City za ta karbi bakuncin PSG a wasa na biyu a ranar Talata 12 ga watan Afirilu.