Wolfsburg ta doke Real Madrid da ci 2-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar Talata ne Real Madrid za ta karbi bakuncin Wolfsburg a wasa na biyu

Wolfsburg ta samu nasara a kan Real Madrid da ci 2-0 a gasar zakarun Turai da suka fafata a ranar Laraba a Jamus.

Wolfsburg din ta fara cin kwallo a bugun fenariti ta hannun Ricardo Rodriguez a minti na 18, sannan ta kara ta biyu a minti na 25 ta hannun Max Arnord.

Kafin su fafata Real Madrid wadda ta doke Barcelona da ci 2-1 a ranar Asabar, ta dauki kofin zakarun Turai sau 10.

Ita kuwa Wolfsburg rashin nasara ta yi a hannun Bayer Leverkusen da ci 3-0 a gasar Bundesliga da suka yi gumurzu a ranar Juma'a.

A ranar Talata ne Real Madrid za ta karbi bakuncin Wolfsburg a wasa na biyu a Bernabeu.