'Za mu kara da Wolfsburg kamar wasan karshe'

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Wannan ne karon farko da kungiyoyin biyu za su hadu a gasar

Kociyan Real Madrid, Zinedine Zidane, ya ce za su buga wasan cin kofin zakarun Turai da Wolfsburg a ranar Laraba tamkar wasan karshe.

Zidane ya ce tuni Madrid ta mance da doke Barcelona da ta yi 2-1 a gasar La Liga a ranar Asabar, domin fuskantar kalubalen da ke gabanbsu.

Ya kuma ce ba za su tsagaita ba, za kuma su kara kwazo, domin za a iya doke su, kuma Wolfsburg za ta iya ba su mamaki.

Zidane din ya kuma ce Wolfsburg ta yi aiki tukuru da ya sa ta kawo matasyin da za su kara a tsakaninsu, kuma wasan zai yi zafi, amma sun shirya tsaf.

Wolfsburg za ta karbi bakuncin Real Madrid a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Laraba a Jamus