Dortmund da Liverpool sun tashi 1-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dortmund za ta ziyarci Anfield a wasa na biyu a ranar Alhamis

Borussia Dortmund da Liverpool sun buga wasa kunnen doki 1-1 a gasar cin kofin Europa wasan daf da na kusa da karshe da suka kara ranar Alhamis a Jamus.

Liverpool ce ta fara zura kwallo ta hannun Origi saura minti tara a tafi hutun rabin lokaci, minti biyu da dawo wa Dortmund ta farke kwallo ta hannun Hummels.

Liverpool za ta karbi bakuncin Borussia Dortmund a wasa na biyu a ranar Alhamis a Anfield.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga a gasar:
  • Ath Bilbao 1 vs Sevilla 2
  • Sporting Braga 1 vs Shakt Donsk 2
  • Villarreal 2 vs Sparta Prague1