U 20: Amuneke ya fara atisaye da 'yan wasa

Image caption Amuneke tsohon kociyan tawagar matasa 'yan kasa da shekara 17 ta Nigeria

Kociyan tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta matasa 'yan kasa da shekara 20, Emmanuel Amuneke, ya fara atisaye da 'yan wasan da suke son buga wa kasar tamaula a ranar Alhamis.

Amuneke na son ya zabi sabbin 'yan wasan da zai hada da guda 30 din da ya gayyata domin buga wasan neman gurbin shiga gasar matasa 'yan kasa da shekara 20 ta Afirka.

An fara yin atisayen ne a ranar 7 ga watan Afirilu zuwa 9 ga watan nan, kafin 'yan wasa 30 da ya gayyata su isa sansanin horon a Abuja.

Nigeria za ta fafata ne da Burundi a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta matasa 'yan kasa da shekara 20 a Bujumbura tsakanin 20 zuwa 22 ga watan Mayu.

Za kuma su kara a wasa na biyu makonni biyu tsakani a Abuja Nigeria.