West Ham za ta karbi bakuncin Arsenal

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Arsenal tana da kwantan wasa daya a gasar ta Premier

Arsenal za ta ziyarci Upton Park domin karawa da West Ham United a gasar cin kofin Premier wasan mako na 33 a ranar Asabar.

A wasan farko da kungiyoyin biyu suka fafata a cikin watan Agusta a gasar, West Ham ce ta doke Arsenal da ci 2-0 a Emirates.

Arsenal wadda take da kwantan wasa daya, tana mataki na uku a kan teburin Premier da maki 58, West Ham kuwa tana matsayi na shida ne a kan teburin da maki 51.

A kakar wasan bana an fitar da Arsenal daga gasar cin kofin zakarun Turai da ta Capital One da kuma ta FA, yayin da West Ham ke cikin gasar cin kofin FA.

Ga sauran wasannin da za a yi a gasar ta Premier:
  • West Ham vs Arsenal
  • Aston Villa vs Bournemouth
  • Crystal Palace vs Norwich
  • Southampton vs Newcastle
  • Swansea vs Chelsea
  • Watford vs Everton
  • Man City vs West Brom