Nigeria na mataki na 14 a iya kwallo a Afirka

Image caption Super Eagles ba ta samu gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a 2017 ba

Nigeria ta yi kasa zuwa mataki na 14 a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a Afirka a jadawalin da Fifa ta fitar na watan Afirilu.

Kungiyoyin da suke goman farko sun hada da Algeria da Cote d'Ivoire da Ghana da Senegal da Masar da Cape Verde da Tunisia da Jamhuriyar Congo da Guinea kuma Congo-Brazzaville.

Sauran kasashen da suke sama a kan Nigeria a jerin jadawalin da Fifa ta fitar a ranar ta Alhamis sun hada da Kamaru da Morocco da kuma Mali.

Nigeria ta samu koma baya ne bayan da ta kasa samun gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a badi a Gabon.

A cikin watan Oktoba ne nahiyar Afirka za ta fara buga wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a shekarar 2018 a Jamus.