Ba ma cikin wadanda za su dauki kofin UEFA

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption City tana mataki na hudu a kan teburin Premier

Kociyan Manchester City, Manuel Pellegrini, ya ce ba sa cikin kungiyoyin da ake hasashen za su dauki kofin zakaraun Turai na bana.

A ranar Laraba ne Manchester City ta tashi wasa 2-2 da Paris St-Germain a wasan farko da suka yi a Faransa a gasar.

Pellegrini ya ce tun farko ba a saka su a cikin jerin kungiyoyin da za su iya lashe kofin ba a bana, tun kafin karawa da PSG har kuma bayan fafatawar.

Wannan ne karon farko da Manchester City ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar cin kofin zakarun Turai tun daga kakar wasan 2011/12.

A ranar Talata ne Manchester City za ta karbi bakuncin PSG a wasa na biyu da za su yi gumurzu a Ettihad.

Da zarar an kammala gasar wasannin bana ne Pep Guardiola zai maye gurbin Manuel Pellegrini a Ettihad.