Marcelo ya yi halin 'yan wasan kwaikwayo — Hecking

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasan da Wolfsburg ta fafata da Real Madrid a gasar zakarun Turai
Kociyan Wolfsburg Dieter Hecking ya bayyana dan wasan baya na Real Madrid Marcelo dive, kamar wani dan wasan kwaikwayo sakamakon abin da ya kira dirama da ya nuna a wasan da Wolfsburg ta ci Madrid din 2-0, a wasan daf da na kusa da na karshe na gasar zakarun Turai.

Dan wasan ya tura kansa ne wajen dan wasan tsakiya na Wolfsburg Max Arnold's midriff, kafin daga bisani ya fadi kasa ya gurje fuskarsa.

An dai bai wa Arnold yalon kati yayin da shi kuma Marcelo ba a yi masa wani hukunci ba.

Dieter Hecking ya ce, "abin da Marcelo ya yi bai dace ba, ya kirkiri wani abu tamkar wasan kwaikwayo. Ban ji dadi ba sam."

Kazalika, shi ma tsohon kociyan Ingila Glenn Hoddle, ya bayyana abin da Marcelo ya yi da cewa abin kunya ne kuma abin takaici.