Ban ji dadin raunin da Henderson ya ji ba — Klopp

Kociyan Liverpool Jurgen Klopp, ya ce bai ji dadin raunin da Jordan Henderson ya ji a gwiwarsa ba, a wasan da suka kara da Borussia Dortmund suka kuma tashi 1-1.

A hutun rabin lokaci ne aka musanya dan wasan da Joe Allen a wasan daf da na kusa da na karshe na gasar Europa, kuma za a yi masa hoton kafa ranar Juma'a don duba yanayin ciwon.

Mista Klopp ya ce, "Wannan ba karamin abu ba ne."

Tun farkon kakar wasan nan Henderson bai buga wasanni ba na tsawon watanni uku sakamakon raunin da yaji a dunduniyarsa lokacin da suke fafatawa da Bournemouth a watan Agustan bara.

Wannan rauni da ya ji na baya-bayan nan na nufin dan wasan ba zai buga wasan da za su yi a Anfield ba a watan Afrilu.