Bana gaggawar samun sabon kontiragi a West Brom - Toni Pulis

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tony Pulis kocin West Brom

Kocin West Brom Tony Pulis, ya ce ba ya gaggawar saka hannu a sabon kontraginsa da kungiyar.

Pulis yana da ragowar shekara daya a wa'adinsa da kulob din, kuma ya ce zai gana da shugaban kungiyar Jeremy Peace a lokacin bazara domin su tattauna makomarsa.

Ya ce, "Zan fi son na zauna da Jeremy mu ci dan kayan makulashe, mu kuma tattauna kan wannan batu. Wannan shi ne abin da nake yi tsawon shekaru."

Kulub din yana matsayi na 11 a teburin gasar Firimiya, kuma suna bukatar maki 13 a wssanin bakwai da za su yi nan gaba domin su tsallake zamowa cikin sahun karshe a teburin Firimiyar kafin wata tafiya da za su yi zuwa birnin Manchester a ranar Asabar.