West Ham: Caroll ya buga 'hat-trick'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andy Caroll wanda ya ci wa West Ham kwallaye uku a jere

Dan wasan kulob din West Ham, Andy Caroll ya ci wa kulob din nasa kwallaye auku, a jere, wato hat-trick, a wasan da suka tashi 3-3 da Arsenal, ranar Asabar.

Tun da farko dai, Arsenal ta zurawa West Ham din kwallaye har biyu ta hannu Mesut Ozil da Alexis Sanchez, kafin daga bisani Andy Caroll din ya farke kwallayen biyu sannan kuma ya dora da ta uku.

Ita ma Arsenal din ta samu ta jefa ta ukun a ragar ta West Ham ta hannun Laurent Koscielny.

Har yanzu dai Arsenal ce ta uku a teburin Premier da maki 59, a inda ita kuma West Ham ta kasance a mataki na 6 da maki 52.