Carroll ya fi kowa cin ƙwallo da ka — Bilic

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A baya dai Andy Caroll ya yi ta fama da jinya.

Kociyan kulob din West Ham United, Slaven Bilic ya ce dan wasansa, Andy Caroll ya fi kowa iya buga tamaula da ka.

Dan wasan mai shekara 27, ya zura kwallaye uku shi a ragar Arsenal shi kaɗai.

Bilic ya ce "idan dai ana maganar zura ƙwallo da ka ne, to zai iya zama wanda ya fi kowa a duniya, ya san aikinsa amma ya kamata ya ƙara jajircewa a kan aikinsa."

Ana sa ran cewa kungiyar wasa ta Ingila za ta gayyaci Andy Caroll domin buga gasar Euro 2016.