Leicester: Jamie Vardie ya ci ƙwallo biyu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jamie Vardy, dan wasan Leicester

Ɗan wasan kulob ɗin Leicester City, Jamie Vardy ya zura ƙwallaye biyu shi kaɗai, a ragar Sunderland, a wasan da suka tashi 2-0, ranar Lahadi.

Hakan ne kuma ya sanya Leicester ɗin ƙarin samun maki a teburin gasar ta Premier.

Yanzu haka, Leicester ce a saman teburin da maki 72 kuma wasanni biyar suka rage mata ta taka.

Ita kuwa Sunderland ta kasance mai matsayi na 18 a teburin kuma maki huɗu ne tsakaninta da fita daga gasar.