Cutar ƙwaƙwalwa na kama 'yan wasa — FA

Hakkin mallakar hoto Press Association
Image caption Tsaffin 'yan wasan kasar Ingila

Hukumar ƙwallon ƙafar Ingila tana son hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya wato Fifa da ta gudanar da bincike kan gaskiyar ko cutar ƙwaƙwalwa da tsoffin 'yan ƙwallo suke samu, tana da alaƙa da wasan na ƙWallo.

Buƙatar dai ta taso ne bayan da aka bayyana cewa mutane uku daga cikin waɗanda suka bugawa Ingila gasar ƙwallon ƙafa ta duniya a 1666 sun kamu da cutar ƙwaƙwalwa ta Alzheimer's.

Tsoffin 'yan wasan dai su ne Martin Peters da Nobby Stiles da kuma Ray Wilson.

Hukumar ta FA dai tana son Fifa ta yi bincike don gano gaskiyar al'amarin.