Leicester: Dole mu ƙara jajircewa - Ranieri

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan wasan Leicester na murnar cin wasa.

Kociyan Leicester City, Claudio Ranieri ya ce dole ne 'yan wasan kulob din su dage, duk kuwa da cewa kungiyar tana ƙara kusantar ɗaukar kofin gasar Premier.

A ranar Lahadi ne dai Leicester ta lallasa Sunderland da ci 2-0, ranar Lahadi.

Ranieri ya ce "ba zan iya faɗa muku irin farin cikina ba."

Sai dai kuma Ranieri ya ƙara da cewa " dole ne 'yan wasanmu su fuskanci ƙalubalen da ke gabansu, su bar magoya baya da iho-ihonsu."