An rage kudin tikitin Leicester zuwa £15,000

Hakkin mallakar hoto Getty

An rage kudin tikitin kallon wasan karshe na Premier a filin wasa na Leicester City zuwa £15,000 ga duk mutam biyu da za su je kallon wasan a tare.

An bayar da sanarwar ne a wani shafin intanet.

Wasan wanda kungiyar zata kara da kungiyar a Everton a ranar 7 ga watan Mayu, wanda akwai yiwuwar Leicester zai yi nasara, an sayar da tikitin a cikin mintuna 90 a ranar Litinin.

Amma kuma a cikin sa'a daya, sai aka rika sayar da tikitin gama-gari a kan £3,000 na mutane biyu kuma sama da haka.

Kungiyar ta ce za ta, "dauki mataki a kan duk wanda ya kuma sayar da tikitin sama da farashin da ake sayar da shi".

Kungiyar Leicester na gaban Tottenham da maki bakwai yayin da ya rage masa wasanni biyar.

Tuni sun yi nasarar samun gurbin zuwa gasar zakarun Turai yayin da suke bukatar yin nasara a wasanni uku domin daukar kofin na Premier