Man City ta yi rawar gani a kofin Turai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Man City ta kai wasan daf da karshe a gasar ta zakarun Turai kuma a karon farko

Manchester City ta kai wasan daf da karshe a gasar cin kofin zakarun Turai, bayan da ta doke Paris St Germain da ci 1-0 a karawar da suka yi ranar Talata.

City ta ci kwallonta ne ta hannun Kevin De Bruyne saura minti 16 a tashi daga fafatawar da suka yi a Ettihad.

A wasan farko da suka kara a Faransa, kungiyoyin biyu kowacce ta zura kwallaye biyu-biyu ne a raga.

Wannan ne karon farko da Manchester City ta taka rawar gani a gasar cin kofin zakarun Turan tun lokacin da ta fara buga wasanninta.