Falcons ta samu tikitin buga gasar Afirka

Hakkin mallakar hoto the nff twitter
Image caption Kamaru ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria, Super Falcons, ta samu tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a bana.

Super Falcons din ta samu gurbin ne bayan da ta doke Senegal da ci 2-0 a fafatawar da suka yi a Abuja a ranar Talata.

Jumulla Nigeria ta ci Senegal 3-1, bayan da suka tashi 1-1 a fafatawar farko da suka yi a ranar 8 ga watan Afirilu a Senegal.

Nigeria ce ke rike da kofin da ta lashe a 2014, kuma tana da shi guda 10 jumulla.

Za a yi wasannin gasar cin kofin Afirka ta mata a Kamaru a cikin watan Nuwamba.