Olympics: Siasia ya gayyaci 'yan wasa 30

Hakkin mallakar hoto TheNFF twitter
Image caption Brazil ce za ta karbi bakuncin wasannin Olympics a bana

Kociyan tawagar matasa 'yan kasa da shekara 23 ta Nigeria, Samson Siasia ya gayyaci 'yan wasa 30, domin yin atisayen tunkarar gasar Olympics da za a yi a bana.

Tawagar ta Nigeria za ta fafata a wasan kwallon kafa a gasar wasannin Olymics da Brazil za ta karbi bakunci a cikin shekarar nan. Sabbin 'yan wasan da aka mikawa goron gayyata sun hada da Godwin Obaje da Julius Emiloju da Ifeanyi Mathew da Kabiru Moshood da kuma Harrison Ibukun.

Ranar Talata ake sa ran halartar 'yan wasan da aka gayyata zuwa otal din Starview dake Gwarinpa a Abuja Nigeria domin fara atisaye a ranar Laraba.

Ga 'yan wasan da Sisia ya gayyato:
 • 1. Emmanuel Daniel (Enugu Rangers)
 • 2. Yusuf Mohammed (Kano Pillars)
 • 3. Daniel Emmanson (Akwa United)
 • 4. Omasteye Alex (First Bank)
 • 5. Sincere Seth (Rhapsody FC)
 • 6. Oduduwa Segun (Nath FC)
 • 7. Obanor Erhun (MFM FC)
 • 8. Ahamefule Chizoba (Abia Warriors)
 • 9. Ndifreke Effiong (Abia Warriors)
 • 10. Chima Akas (Enyimba FC)
 • 11. Timothy Danladi (Katsina United)
 • 12. Stanley Okorom (MFM FC)
 • 13. Harrison Ibukun (Akwa United)
 • 14. Ubong Ekpai (Akwa United)
 • 15. David Itoho (Nath FC)
 • 16. Kabiru Moshood (Ikorodu United)
 • 17. Bright Onyedikachi (FC IfeanyiUbah)
 • 18. Ifeanyi Mathew (Kano Pillars)
 • 19. Tiongoli Tonbara (Bayelsa United)
 • 20. Olisah Ndah (Rivers FC)
 • 21. Julius Emiloju (MFM FC)
 • 22. Joseph Osadiaye (Enyimba FC)
 • 23. Daniel Etor (Enyimba FC)
 • 24. Austine Dimgba (Sunshine Stars)
 • 25. Ezekiel Mbah (Kano Pillars)
 • 26. Abdulrahman Taiwo (Kwara United)
 • 27. Godwin Obaje (Wikki Tourists)
 • 28. Kufre Ebong (Akwa United)
 • 29. Uchenna Agha (Freestans FC)
 • 30. Godwin Aguda (Rangers FC)