UEFA: Real Madrid ta kai wasan daf da karshe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ronaldo ne ya ci dukkan kwallaye ukun

Real Madrid ta kai wasan daf da karshe a gasar cin kofin zakarun Turai, bayan da ta doke Wolfsburg da ci 3-0.

Cristiano Ronaldo ne ya ci wa Real Madrid dukkan kwallayen uku, inda ya ci ta farko a minti na 16 da fara wasa, ya kuma kara ta biyu a minti na 17.

Ronaldo tsohon dan wasan Manchester United, ya ci kwallo ta uku kuma wadda ta bai wa Madrid damar kaiwa wasan gaba a gasar saura minti 13 a tashi daga karawar.

A wasan farko da suka yi a Jamus, Wolfsburge ce ta doke Madrid da ci 2-0.

Real Madrid ta lashe kofin zakarun Turai sau 10 jumulla.