An fitar da Barca daga gasar zakarun Turai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona tana matsayi na daya a kan teburin La Liga

Atletico Madrid ta doke Barcelona da ci 2-0, ta kuma fitar da ita daga gasar cin kofin zakarun Turai ta bana a fafatawar da suka yi ranar Laraba.

Atletico ta ci kwallon farko ne ta hannun Antoine Griezmann kafin a tafi hutun rabin lokaci, kuma shi ne dai ya kara ta biyu a bugun fenariti daf da za a tashi wasan.

Atletico ta ci Barcelona kwallaye 3-2 a karawa biyu da suka yi, wanda suka tashi 1-1 a gidan Barcelona a ranar Talata.

Barcelona ce ke rike da kofin bara, kuma tana da shi guda biyar da ta lashe.

A gasar La Liga Barcelona ce ke mataki na daya da maki 76, sai Atletico Madrid ta biyu da maki 73, inda Real Madrid ke matsayi na uku da maki 72.