United ta kai wasan daf da karshe a kofin FA

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United ta lashe kofin FA sau 11, kuma rabon da ta dauki kofin tun 2004

Manchester United ta kai wasan daf da karshe a gasar cin kofin kalubale, bayan da ta doke West Ham United da ci 2-1 a Upton Park ranar Laraba.

United din ce ta fara cin kwallo ta hannun Rashford bayan da aka dawo daga hutu, sannan Fellaini ya ci ta biyu a karawar.

Saura minti 11 a tashi daga wasan ne West Ham United ta ci kwallo ta hannun Tomkin.

A wasan farko da suka buga a gasar tashi suka yi kunnen doki 1-1 a Old Trafford.

West Ham za ta kara karbar bakuncin Manchester United a gasar cin kofin Premier a ranar 10 ga watan Mayu a Upton Park.