West Ham za ta kara da Man United

Image caption Man United da West Ham tashi suka yi 1-1 a Old Trafford

West Ham United za ta karbi bakuncin Manchester United a wasa na biyu na cin kofin kalubale wasan daf da na kusa da karshe a ranar Laraba.

A wasan farko da aka buga a Old Trafford kungiyoyin biyu tashi suka yi kunnen doki 1-1.

Kungiyoyin biyu za kuma su sake karawa a Upton Park a wasan gasar cin kofin Premier a ranar 10 ga watan Mayu.

Rabon da Manchester United ta lashe kofin FA tun a shekarar 2004, wanda ta lashe kofin sau 11 jumulla.