Nasarawa United ta doke Giwa FC 3-1

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Kwantan wasanni biyu aka buga a gasar ta Firimiyar Nigeria

Nasarawa United ta doke Giwa FC da ci 3-1 a kwantan wasan gasar Firimiyar Nigeria da suka kara a ranar Laraba.

Nasarawa ce ta fara zura kwallo a minti na 19 da fara wasa ta hannun Abdulrahman Bashir, Giwa ta farke kwallo ta hannun Aminu Mbai a minti na 30.

Abdulrahman Bashir ne ya kara ci wa Nasarawa kwallo na biyu, sannan Aminu Kadir wanda ya shiga wasan daga baya ya kara ta uku a raga.

Wasan da suka buga shi ne na mako na uku da ba su fafata ba, sakamakon gasar cin kofin zakarun Afirka da Nasarawa ta buga a lokacin.

Ita kuwa Sunshine Stars ta samu maki uku a gasar, bayan da ta doke Enyimba da ci 2-1 a kwantan wasan mako na ukun da suka yi.

Gobe ne za a buga kwantan wasan mako na bakwai tsakanin Warri Wolves da Abia Warriors.