Enrique ya dauki laifin fitar da Barca

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption ''Na dauki laifi dari bisa dari''

Kocin Barcelona Luis Enrique, ya dauki laifin fitar da Barcelona daga gasar Zakarun Turai a matakin wasan dab da na kusa da karshe.

Ya ce, ''kungiyar tana cikin wani hali na tsaka-mai-wuya kuma ta shiga yanayi na kasa cin kwallaye''.

Abokan hamayyar masu rike da kofin a Spaniya Atletico Madrid su ne suka fitar da su daga gasar da jumullar kwallaye 3-2.

A karawar da suka yi jiya Atleticon ta ci su biyu ba ko daya, yayin da a haduwarsu ta farko a gidan Barcelona Nou Camp Zakarun La Ligan ne suka ci Atleticon 2-1.

Kociyan ya ce, ''ni ya kamata a dora wa alhakin rashin nasarar kashi 99.9, a'a dari bisa dari ma ya kamata a dora min.

Wannan shi ya sa nake matsayin mai horad da su, wanda nauyi ya fi rataya a wuyansa. Dole ne dukkaninmu mu tashi tsaye.''

Antoine Griezmann ne ya ci wa Ttletico duka kwallaye biyun a filin wasansu na Vicente Calderon, yayin da Messi ya kasa ci wa kungiyarsa kwallo a karo na biyar a jere.

Wannan shi ne karo na uku a shekara 11 da Barcelona ta kasa zuwa wasan kusa da karshe na gasar kofin Zakarun Turai.

Yanzu dai maki uku ne tsakanin Atletico da Barcelona wadda ke mataki na daya a teburin La Liga, amma kuma Barcan ta yi rashin nasara a wasanninta uku daga cikin hudu a gasannin da suke yi.

Kociyan ya ce, '' dole ne mu tsaya mu natsu kuma mu yi tunani cewa har yanzu muna da sauran gasa biyu a gabanmu.