An cire alkalin wasa saboda Leicester

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Alkali Kevin Friend mai goyon bayan kungiyar Leicester ne

Hukumar gasar Premier ta cire Kevin Friend wanda a da aka tsara zai yi alkalancin wasan Tottenham da Stoke City na ranar Litinin, saboda shi mai goyon bayan kungiyar Leicester ne, wadda ke matsayi na daya a tebur.

Kungiyar Tottenham ita ce ke bin Leicester City a tebur da bambancin maki bakwai tsakaninsu yayin da ya rage wasanni biyar a kammala gasar ta bana.

Hukumar alkalan wasa ta Ingila (PGMOL) ba ta sanya Friend, wanda ke zaune a Leicester, kuma yake zuwa kallon wasansu a matsayin kashin kansa, ya yi alkalancin wasannin kungiyar.

Hukumar ta ce bisa la'akari da lokaci da kuma matsayin wasan ya sa aka sauya shi, a wasan da za a yi na Tottenham da Stoke City.

A madadinsa yanzu an sanya Neil Swarbrick daga Preston ya yi alkalancin wasan a Stoke, shi kuwa Friend din zai kula da wasan Newcastle da Manchester City a ranar Talata.