Sunderland ta ci Norwich kwallaye 3-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Defoe da Borini sun taka rawar gani a wasan da Sunderland ta doke Norwich

Norwich ta yi rashin nasara har gida a hannun Sunderland da ci 3-0 a gasar Premier wasan mako na 34 da suka kara a Carrow Road ranar Asabar.

Sunderland ta ci kwallon farko ta hannun Jermain Defoe a bugun fenariti, bayan da dan wasan Norwich ya yi wa Fabio Borini keta a cikin da'ira ta 18 kafin a ta fi hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo ne daga hutu sai Sunderlnad ta ci kwallo ta biyu ta hannun Jermain Defoe, sannan Duncan Watmore ya kara ta uku a raga daf da za a tashi daga wasan.

Sunderland wadda take da kwantan wasa daya, tana da maki 30 a mataki na 18 a kan teburi, yayin da Norwich wadda ta yi wasanni 34 tana matsayi na 17 a kan teburi da maki 31.