Liverpool ta ci Bournemouth 2-1

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Liverpool za ta yi wasan gaba da Everton a Anfield

Bournemouth ta yi rashin nasara a hannun Liverpool da ci 2-1 a gasar Premier wasan mako na 34 da suka fafata a ranar Lahadi.

Liverpool ta ci kwallayen ne ta hannun Firmino da kuma wadda Sturridge ya kara ta biyu daf da za tafi hutun rabin lokaci.

Bournemouth ta zare kwallon daya ta hannun King daf da za a tashi daga fafatawar.

Liverpool din tana matsayi na bakwai a kan teburin Premier, inda Bournemouth ke mataki na 13 da maki 41.

Liverpool wadda ta kai wasan daf da karshe a gasar Europa, za ta buga wasan Premier na gaba ne da Everton a Anfield.

Ita kuwa Bournemouth za ta karbi bakuncin Chelsea a wasan mako na 35 da za su fafata.