"Aguero ya fi kowa iya cin kwallaye a Premier"

Hakkin mallakar hoto Reax Features
Image caption Aguero ne ya ci Chelsea kwallaye uku a Stamford Bridge

Kociyan Manchester City, Manuel Pellegrini, ya ce Sergio Aguero, shi ne gwani wajen iya cin kwallaye a gasar Premier.

A ranar Asabar ne Aguero ya ci Chelsea kwallaye uku a gasar mako na 34 da suka yi buga, kuma jumulla ya ci 21 a gasar.

Hakan ne ya kuma sa dan wasan tawagar kwallon kafa ta Argentina ya ci kwallaye 99 a kakar wasanni biyar da ya buga wa City tamaula jumulla.

Wannan kuma shi ne karo na biyu da Aguero ya ci kwallaye sama da 20 a gasar ta Premier, domin a bara 26 ya ci.

Sai dai kuma duk da kwazon da dan kwallon ke nunawa a bana, baya cikin jerin 'yan wasan da za a zabi wanda ya fi yin fice a gasar Premier da ake buga wa.

Pellegrini ya ce Aguero ya na zama raba gardama idan yana buga wasa a koda yaushe a kuma duk mako, babu wani dan wasan da ya kai shi iya cin kwallo a Premier.