Ba zan kira Carroll don ya ci kwallo 3 ba - Hodgson

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Carroll ne ya ci Arsenal kwallaye uku a gasar Premier

Kociyan tawagar kwallon kafa ta Ingila, Roy Hodgson ya ce Andy Carroll bai cancanci ya buga wa kasar gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a bana ba.

Hodgson ya ce ana ta kiraye-kirayen a gayyaci Carroll cikin tawagar Ingila, bayan da ya ci kwallaye uku a karawar da suka tashi 3-3 da Arsenal a wasan Premier.

Kocin ya ce a duk lokacin da dan kasar Ingila ya ci kwallo a wasa, sai kaji ana ta cewa mai ya sa baya buga wa tawagar wasanni.

Hodgson ya ce ba zai ba shi goron gayyata zuwa buga wa tawagar kwallon kafar Ingila tamaula ba don kawai ya ci kwallaye uku a wasa.

Andy Carroll tsohon dan wasan Newcastle da Liverpool ya ci wa Ingila kwallaye biyu a wasanni tara da ya buga wa tawagar.

Sai dai kuma rabon da ya yi mata wasa tun cikin watan Oktoban shekarar 2012.