Bana son komawa Liverpool- Balotelli

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mario Balotelli ya ce baya son komawa Liverpool

Mario Balotelli ya ce baya son komawa Liverpool idan wa'adin aron sa da AC Milan ta yi ya kare a kakar bana.

Dan wasan mai shekara 25, ya sake komawa tsohon kulob din sa ne a matsayin aro daga Liverpool a watan Augustan da ya gabata.

Balotelli ya yi ta kokarin dawowa kan ganiyarsa inda ya ci kwallaye uku a cikin wasanni 19, kuma ya yi rawar gani a wasanni biyun da kungiyar AC Milan ta yi.

Dan wasan ya ce " ina son na cigaba da kasancewa da AC Milan, ba na jin dadin zamana a Liverpool kuma ba na son kmawa can".

Balotelli wanda tsohon dan wasan kulub din Manchester City ne, an saka shi tunda farkon wasan da AC Milan ta yi a ranar Lahadi wanda ta ci 1-0.

Balotelli ya cigaba da takarawar gani har bayan wasan da Juventus ta yi nasara a kan AC Milan da ci 2-1.