Messi ya zura kwallo 500

Dan wasan Barcelona Lionel Messi ya zura kwallo ta 500 a tarihinsa na buga kwallon kafa.

Messi ya zura kwallonsa ta 500 a wasan da Valencia ta doke Barcelona da ci 2-1, lamarin ya Barcelona ya sha kashi sau uku a jere a karon farko a gasar La Liga tun daga shekarar 2003.

Barcelona ce ta fara cin gida ta hannun Ivan Rakitic a minti na 26 da fara wasan, sannan Santiago Mina ya ci wa Valencia kwallo ta biyu.

A lokacin da Messi ya ci kwallo a wasan da Barcelona ta doke Arsenal a Gasar Zakarun Turai ranar 16 ga watan Maris, mutane ba su yi tsammanin zai kwashe fiye da wata daya bai zura kwallo ba.