Moyes na son komawa Villa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption David Moyes na son komawa Aston Villa

David Moyes ya ce ya na sha'awar zama kociyan Aston Villa kodayake har yanzu kulob din bai tuntube shi ba.

Kusan watanni shida ke nan da kulob din Real Sociedad ya kore shi, Yanzu Moyes na son komawa harkokin fagen wasannin kwallon kafa kuma hankalinsa ya fi karkata ya tafi Villa.

Kociyan mai kimanin shekaru 52 da haihuwa,ya kalli wasan kungiyar kwanannan, kuma a shirye yake a tattauna da shi, sai dai kuma yana sane da cewa batun kasafin kudin kungiyar na shekara mai zuwa zai iya kawo masa jinkiri.

Sai dai kuma masu sharhi kan harkokin wasanni na ganin cewa wata kila Nigel Pearson kungiyar za ta dauka.

Tsohon kociyan Leicester City ba shi da wani kulob har yanzu, tun bayan da ya bar ta a watan Yunin da ya gabata, bayan da ya kai su wasan Premier.