Aston Villa ta dakatar da Agbonlahor

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Aston Villa za ta koma buga gasar Championship

Aston Villa ta dakatar da Gabby Agbonlahor, za kuma ta yi binkice kan dabi'un dan wasan.

A rahotannin da jaridu suka wallafa, an nuna dan kwallon yana rike da gwanganin kayan maye a wajen fati a daren da aka fitar da Aston Villa daga gasar Premier.

Tun a baya, kungiyar ta daina saka Agbonlahor a wasanni, bayan da ta ce ba shi da kuzari.

A ranar Asabar aka tabbatar da barin Villa daga buga gasar Premier, bayan da Manchester United ta doke ta da ci 1-0 a wasan mako na 34.