'Yan wasa ne suka yaudari Mourinho - Fabregas

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fabregas da tsohon kociyan Chelsea, Jose Mourinho

Cesc Fabregas ya ce abin da ya sa Mourinho ya kasa tabuka rawar gani a Chelsea, saboda yarda da ya yi da 'yan wasansa dari bisa dari.

Fabregas ya ce 'yan wasa ne suka yaudari Mourinho duk da kara musu lokacin hutun da ya yi bayan da suka lashe kofin Premier bara.

Dan wasan mai shekara 28, tsohon dan kwallon Arsenal da Barcelona ya kara da cewa yana martaba kociyan.

Fabregas ya fada wa Sky Sports cewar matsalar da aka samu ita ce Mourinho ya amince da yan wasansa sosai, ya kuma sa sun huta saboda lashe kofin Premier da suka yi.

Cikin watan Disamba ne Chelsea ta sallami Mourinho daga aiki ta kuma maye gurbinsa da Guus Hiddink.