Hukumar Firimiya ta hukunta Giwa FC

Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption Giwa FC za ta buga wasanni uku a gasar ta Firimiyar Nigeria a Ilori

Hukumar gudanar da gasar cin kofin Firimiyar Nigeria ta ci tarar Giwa FC kudi naira miliyan biyar, za kuma ta buga wasanninta uku na gaba a gasar a Ilori.

Hukumar ta yanke wannan hukuncin ne sakamakon hatsaniya da ta barke a wasan mako na 12 a gasar da Giwa ta karbi bakuncin Rangers a ranar Lahadi a Jos.

Hukumar ta kuma ce Giwa FC za ta karasa mintunan wasan da suka rage a Abuja kafin alkalin wasa ya hura tashi a karawar da suka yi da Rangers din.

Haka kuma za ta ci gaba da yin wasanninta a gida ba tare da 'yan kallo ba idan ta gama hukuncin da aka yanke mata, amma an ba ta damar daukaka kara.

Kungiyar tana mataki na 16 a kan teburin gasar da maki 14, bayan da ta yi wasanni 11.