An fitar da Mazembe daga kofin zakaru

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption John Toshack kociyan Wydad ta Casablanca

An fitar da mai rike da kofin zakarun Afirka TP Mazembe daga gasar bana, bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 da Wydad ta Casablanca.

Mazembe ce ta fara cin kwallo ta hannun Salif Coulibaly a minti na 28 da fara tamaula.

Wydad din ta farke kwallon ne daf da za a tashi daga fafataar ta hannun Reda Hajhouj.

Da wannan sakamakon Wydad din ta ci Mazembe 3-1 a haduwa biyu da suka yi.

A ranar 24 ga watan Mayu, ake sa ran raba jadawalin wasannin rukuni na gasar ta zakarun Afirka a Masar.